An cimma yarjejeniya kan bututun iskar Gaz
July 22, 2021Talla
Cimma yarjejeniyaar ta kawar da fargaba game da dogaron kasashen Turai kan makamashin Gas na Rasha, sai dai kuma har yanzu akwai wadanda ke nuna shakku akan batun.
A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, Amirka da Jamus sun jaddada kudirinsu na daukar mataki akan Rasha idan ta yi kokarin amfani da batun bututun a matsayin makami a siyasance.
An cimma yarjejeniyar ce kwanaki kalilan bayan ziyarar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai wa shugaban Amirka Joe Biden kuma watanni biyu kafin ta sauka daga karagar mulki.
Kasashen na Jamus da Amirka sun kuma yi alkawarin taimakawa kasashen Ukraine da Poland wadanda aikin shifida bututun ya kewaye su.
Za kuma su taimakawa kasashen da fasahar sabbin dabarun makamashi.