Jamus tana mayar da mutane Afghanistan
July 23, 2025Ministan cikin gidan Jamus Alexander Dobrindt ya baiyana gamsuwa da nasarar mayar da wani rukuni na masu laifi yan Afghanistan zuwa kasarsu a cikin wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata. Jirgin da ya mayar da mutanen wanda ya tashi daga Leipzig zuwa Kabul yana dauke da mutane 81 duk maza wadanda Jamus ta nemi su bar kasarta.
Karin Bayani: Maharin birnin Munich ya amsa laifinsa
A ra'ayinsa Dobrindtt ya ce kawancen Jam'iyyun CDU/CSU da kuma SPD wadanda ke kan mulki tun watan Mayu sun cika alkawari. Hasali ma ya ce wannan yana rubuce a cikin a jadawalin yarjajaeniyar kawancen gwamnatin cewa za a mayar da 'yan Afghanistan da yan Siriya, amma za a fara ne da mutanen da suke masu laifi da ke da matukar hadari.
Tun ma dai tsohuwar gwamnatin da ta shude aka fara jigilar mayar da mutanen ta jirgin sama a karkashin tsohuwar gwamnatin kawance da ta kunshi Jam'iyyun SPD da FDP da kuma Greens a watan Augustan 2024.
Da yake tsokaci kan manufar da aka kaddamar, Dobrindt ya ce an bukaci kasashe su karbi mutanensu. Sai dai ga kasar Afghanistan lamarin na da sarkakiya da wuyar sha'ani saboda Jamus ba ta amince da gwamnatin Taliban ba a karkashin dokokin kasa da kasa.
Gwamnatin mai kaifin kishin Islama ta yi kaurin suna wajen tauye hakkin mata da yan mata tun bayan da ta dawo kan karagar mulki a watan Augustan 2021. Yanayin rayuwar al'umma ta tabarbare bayan shekaru 20 da kasar ta shafe tana yakin basasa. Yunkurin dora kasar kan turbar dimukuradiyya bisa tsarin yammacin turai a karkashin tsarin amfani da matakin soji da Amurka ta jagoranta ya ci tura wanda ya kai ga janyewar sojojin kasa da kasa.
Tun ma dai kafin 'yan Taliban su sake dawowa kan mulki aka fara mayar da 'yan Afghanistan gida. Lamarin ya kasance mai sarkakakiya a lokacin saboda tabarbarewar sha'anin tsaro a kasar a wancan lokaci. Har yanzun ma akwai sarkakiya sakamakon yawan taka hakkokin dan Adam.