Jamus ta zaftare tallafin raya kasashen ketare
July 1, 2025Jamus ta zaftare tallafin ne a kasafin kudin shekara ta 2025. Ma'aikatar Tattalin Arziki da Ci gaba na Jamus za ta karbi euro biliyan €10.3 kwatankwacin Dalar Amurka biliyan ($12.1), kasa da abin da aka ware wa Ma'aikatar a 2024.
Karin bayani: Jamus za ta bai wa Afirka rigakafin cutar Kyandar Biri
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Agajin Jinkai a Jamus wanda kuma ke wakiltar kungiyoyi sama da 140 a kasar, Michael Herbst, ya ce matakin gwamnatin Jamus zai jefa rayuwar al'umma da dama cikin tashin hankali a daidai lokacin da mutane sama da miliyan 100 ke tsananin bukatar agajin jinkai musamman a kasashen da ke fama da yake-yake.
Karin bayani: Jamus ta shirya bai wa Siriya tallafin kudade
Matakin gwamnatin Jamus na zuwa ne a daidai lokacin Shugaban Amurka Donald Trump ya zaftare tallafin raya kasashe da kashi 80% bisa 100.