Jamus ta soki hanyar da ake bi na warware basukan Turai
August 24, 2011Talla
Shugaban ƙasar Jamus Christian Wulff ya soki gwamnatocin kasashen da ke amfani da kuɗin Euro bisa yadda suke tafiyar da batun basukan dake kansu. Wulff yace a tsammaninsa matakin sayan basukan da kasashen Turai suka bi, ba kekkewan tsari bane. Babban bankin ƙasashen dake amfani da kuɗin Euro ya fara sayan basukan da ake bin wasu kasashe tun a bara. A baya dai an haramta yin hakan, domin gudun kada a ƙeta yanci da siyasar ƙasashen. Shugaban na ƙasar Jamus ya kuma bayyana cewa gwamnatocin Turai sun yi sakaci har sanda lokaci ya kure, kafin su fara shirin tsuke bakin aljihu, da kawo sau-sauye. Abinda kuma yace shine ya tilastawa babban bankin ƙasashen wuce iyakar da aka ƙayyade masa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu