SiyasaAsiya
Jamus ta kori jami'an diflomasiyyar Rasha
December 16, 2021Talla
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta ce wannan kisan gilla da kotu ta tabbatar cewa Rasha ce ta kitsa shi na cikin munanan laifuka a bisa dokokin Jamus.
A ranar Laraba ce dai kotun ta Berlin ta yanke wa wani dan kasar Rasha Vadim Krasikov hukuncin daurin rai-da-rai bayan samunsa da kisan wani dan kasar Jojiya a wani wurin shakatawa a nan Jamus. Kotun ta ce mahukuntan Moscow ne suka shirya kisan gillar na mutumin na Jojiya da ya zo neman mafaka.