Jamus ta jefa kayan abinci da magunguna ga al'ummar Gaza
August 2, 2025Dakarun sojin saman Jamus sun jefa kayan agaji na abinci da magunguna ta sama ga al'ummar Gaza, masu fama da kangin yunwa, wanda nauyin kayan ya kai kusan tan 10 a wannan Asabar, bayan tasowar jirgin daga Jordan, dauke da kunshin kaya kimanin 22.
Rundunar sojin wadda aka fi sani da Bundeswehr, ta ce a ranar Lahadi jiragen agajin za su ci gaba da jefa kayan masarufin ga mabukata, domin saukaka wa al'ummar Gaza mawuyacin halin da suke ciki.
Rundunar sojin Isra'ila wadda ita ce ke kula da rarraba kayan jin kan, ta ce a Asabar kadai an jefa wa al'ummar Gaza kayan agaji kimanin kunshi 90, ta hannun kasashen Faransa da Masar da Jordan da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana Gaza a matsayin yankin da ke dab da fadawa mumman kangi na yunwa da galabaita.
Karin bayani:Jamus ta fara kai agaji ta sama zuwa Zirin Gaza
Tuni kungiyar Hamas ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya da makamai a yankin Gaza har sai an amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta, a wani mataki na nuna turjiyar kawo karshen yakinta da Isra'ila.
Hamas wadda ke rike da ikon yankin Gaza tun a shekarar 2007, kuma take faman yakin tayar da kayar baya ga Isra'ila tsawon lokaci, ta ce birnin Kudus take muradin ganin ya zama cibiyar kasar Falasdinu, sannan za ta amince da zubar da makamanta, kamar yadda ta sanar.
Karin bayani:Jakandan Amurka ya ziyarci wajen rabon abinci a Gaza
A ranar Talata kasashen da ke shiga tsakani don sulhunta wannan rikici wato Qatar da Masar suka amince da kudurin kasashen Faransa da Saudi Arebiya, na share fagen samar da kasashe biyu 'yantattu, wato Isra'ila da Falasdinu.
Ya zuwa wannan lokaci, duk wani kokari na ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 60 tsakanin Isra'ila da Hamas, tare da sakin fursunonin da Hamas din ta yi garkuwa da su abin ya ci tura, bayan da bangarorin biyu da ba sa jituwa da juna suka ja daga.