Jamus ta fara kai agaji ta sama zuwa Zirin Gaza
August 2, 2025Rundunar sojin Jamus ta fara gudanar da aikin jefa kayan gaji ta sama a Zirin Gaza. Ma'aikatar tsaron Jamus da ke Berlin fadar gwamnatin kasar ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce jiragen rundunar sojin sama sun aje kunshin tallafi 34 dauki da tan 14 na abinci da kuma magunguna.
Karin bayani: Isra'ila ta fara barin motocin agaji shiga Gaza
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Zirin na bukatar tallafin tan dubu 62 na abinci a duk wata domin mutane su rayu. Isra'ila dai na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya kan matakin ta a Gaza wanda ya kai ga samun rahotannin matsanancin karancin abinci a Zirin. Tun a ranar Lahadi Isra'ila ta aminci da shigar da agaji ta kasa da sama, inda kasashe irinsu Jordan da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka yi ta jefa kayan agaji ta sama. Sai dai a cewar ministan tsaron Jamus, Moris Pistorius kai tallafi ta sama ba zai yi wani babban tasiri ba.