Jamus ta bukaci tattaunawa da Amurka kan haraji
April 2, 2025Ministan kudin na Jamus Jörg Kukies ya shaida wa DW cewa karin harajin zai shafi Amurka saboda motoci za su kara yin tsada a kasar ciki har da motocin da kamfanonin Jamus ke kerawa a Amurka.
Ya ce kamfanonin Jamus masu kera motoci sun fi kera motoci a Amurka fiye da yadda suke shigo da motocin daga Turai a saboda haka tasirin zai fi radadi a Amurka.
Sai dai kuma Ministan ya ce gwamnatin Jamus za ta dauki sanarwar a matsayin wata dama ta tattaunawa a kan batun.
Ya ce gwamnatin Jamus na fatan tuntubar zuna za ta ci gaba da wanzuwa a dangantaka da gwamnatin Trump kuma sakamakon zai biyo baya zai kasance na ragin harajin yana mai cewa a tattaunawar da ake yi ta kafa sabuwar gwamnati a Jamus, jam'iyyun kawancen na SPD, CDU da CSU suna bayar da shawarar cinikayya ba tare da shinge ba tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai da Amurka.