Jamus ta bude ofishin jakadancinta a Syria
March 20, 2025Talla
Kasar ta Syria dai na fuskantar tarin matsalolin jinkai da na tsaro daidai lokacin da ta kara karfin damarar saita al'amura bayan kawo karshen jagorancin hambararren Shugaba Bashar al-Assad cikin watan Disamba.
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ce ta jagoranci sake bude ofishin jakadanci yau a birnin Damascus.
Yanzu dai ofishin jakadancin na da ma'aikata kalilan ne, sai dai sannu a hankali za su ci gaba da karuwa yayin da al'amura ke kara ingantuwa.
Jamus dai na daga cikin kasashen da ta karbi dubban 'yan Syria a cikin shekaru 10 da suka gabata saboda guje wa yakin kasar.