Jamus na fuskantar karancin ma'aikata a Bundeswehr
March 12, 2025Rahoton mai shafuka 183 da kwamishinan kula da harkokin soja a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ya gabatar ya lissafo matsaloli masu yawa da za a iya gyarawa, ciki har da batun gyaran dakunan kwana da ke cikin bariki da karancin makamai da ma na sojojin. A halin yanzu dai, akwai sojoji kusan dubu 181 da ke aiki a rundunar ta Bundeswehr. Idan aka kwatanta da manufar da ake so ta sojoji adadin yayi kadan, sannan ana samun raguwar sojojin kana kuma kayan aikinta na tsufa. Rundunar ta Bundeswehr na daukar sababbin ma'aikata dan radin kansu ta hanyar janyo hankulansu da sanya manya-manyan hotunan talla a biranen Jamus, tare da nuna rayuwar sojoji ta yau da kullum a kafafen sada zumunta. Wannan yana sanya karuwar matasa masu yawa, wadanda ke sha'awa da neman zama sojin a Jamus a shekara ta 2024.
Amma da yawa daga cikin sababbin daukar sun daina aikin, inda daya cikin mutane hudu da suka shiga rundunar ta Bundeswehr, ke barin aikin cikin watanni shida na gfarko. Yanzu haka dai ana tafka muhawara a kan ko za a sake shigar da tsarin daukar sojoji ya zama dole a Jamus, kamar a shekara ta 2011, sai dai kwararu dai na ganin akwai wahala a iya aiwatar da wannan shiri. Duk da cewar babu isassun dakuna, ga rashin isassun kayan aiki ga kuma rashin isassun masu horarwa, kayan aikin na rundunar Bundeswehr sun dan inganta a 2024 a cewar rahoton Kwamitin Kula da Sojoji na Majalisar. Wannan ya shafi duka kayan aikin sojoji da kuma samar da tsarin makamai na zamani gaba daya, sakamakon samar da asusu na musamman na Euro biliyan 100 ga rundunar ta Bundeswehr bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a shekarar 2022.