An kai hari da wuka tashar jirgin kasa a Jamus
May 23, 2025Talla
'Yan sanda sun tabbatar da kama wanda ake zargi da kai harin, amma babu karin bayani kan maharin da kuma dalilin kai farwa mutane. Jaridar 'Bild' wacce ta fara buga labarin, ta ce an zuba jami'ai a ciki da wajen filin jirgin kasan don gudanar da bincike bayan faruwar lamarin.
'Yansandan Jamus na farautar wani mahari
A baya-bayan nan ana yawan samun kai hare hare da wuka kan jama'a a Jamus, matakin da ya sa gwamnatin ke tsauarara matakan bincike tare da dakile kwarar baki ta kan iyakar kasar.