Jamus: Merz ya gaza samun amincewar majalisa
May 6, 2025Rashin samun kuri'u shida ne suka dakatar da jagoran jam'iyyar CDU din cimma burinsa a wannan Talata. Merz wanda ya jam'iyyarsa ta kayar da jam'iyyar SPD a zaben watan Fabrairu ya samu kuri'u 310 a kuri'ar amincewa a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban gwamnati da 'yan majalsiar Jamus suka kada a Talatar nan. Sai dai doka ta tilasta cewa sai dan siyasa ya samu kuri'u 316 daga cikin mambobin majalisa 630 kafin ya zama shugaban gwamnati.
Jam'iyyun CDU, CSU da SPD da Merz ya kulla kawance da su domin samun kuri'un da yake bukata a kuri'ar ta yau, na da mambobi 328. Amma kawo yanzu babu wani kwakkwaran dalilin da ya hana gaba daya mambobin wadannan jam'iyyu amincewa da shi kamar yadda suka yi alkawari.
Kuri'ar da 'yan majalisar Jamus din suka kada a Talatar nan, ita ce ta farko, za su iya sake kada wata kuri'ar. A bisa dokokin kasar, yanzu 'yan majalisa na da kwanaki 14 domin su sake kokarin zaben sabon shugaban gwamnati, daga nan kuma, shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier, zai samu damar tabbatar da wanda aka zaba ko kuma rusa majalisar gaba daya, idan 'yan majalisar suka gaza zabar wani sabon shugaban gwamnati,