Mai Merz ya yi a kwanaki 100 a kan mulki?
August 4, 2025Sai dai kuma, kawancen gwamnatinsa na fuskantar barazanar rikici kan kotun tsarin mulki. A lokacin da Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta zauna a ranar shida ga watan Mayu, domin zaben shugaban Jam'iyyar na CDU Friedrich Merz a matsayin shugaban gwamnati, wasu manazarta sun yi bayani a kan dama ta karshe ga dimukuradiyyar kasar. Samun wata shekara ta jayayya kamar yadda ta auku a karkashin tsohuwar gwamnatin da ta shude ta SPD da Greens da kuma FDP zai farraka al'umma, inda a hannu guda ake da 'yan ra'ayin rikau a daya bangaren kuma da karuwar fusata kan shugabanni da ke neman kai wa kololuwa. A zaben da ya gabata a watan Fabrairun 2025, jam'iyyar AfD mai ra'ayin matsanancin kishin kasa da kyamar baki ta rubanya kokari a sakamakon da ta samu na sama da kaso takwas cikin 100.
Karin Bayani: An rantsar da Merz shugaban gwamnatin Jamus
Yanzu masu ra'ayin 'yan mazan jiya da ke kewaye da Friedrich Merz da masu sassaucin ra'ayi na SPD na son hada hannu, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Sai dai tun tashin farko aka fara cin karo da matsaloli, inda da farko Merz ya gaza a yunkurinsa na zama shugaban gwamnati. Kuri'u shida suka gaza masa na 'yan jam'iyyarsa da suka yi masa rowa, abin da bai taba faruwa ba ga wani dan takarar shugabancin gwamnatin Jamus kafin Merz. Sai a zagaye na biyu na kuri'ar a ranar shida ga watan Mayun 2025, Merz ya tsallake rijiya da baya. A cikin kusan kwanaki 100 da suka gabata, Merz ya kasance ja gaban manufofin harkokin waje. Jim kadan bayan zabensa, ya kai ziyara mai muhimmanci zuwa Ukraine tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron da firaministan Birtaniya Keir Starmer. Yayin ziyarar tasu, ya tabbatarwa da shugaba Volodymyr Zelensky goyon bayansa.
Sannan a farkon watan Yuni, ya ziyarci shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House. Sabanin wasu shugabanni da dama, Trump ya karrama shi kwarai. Merz ya kuma samu tagomashi a taron kolin shugabannin kungiyar Tarayyar Turai EU da kuma taron shugabannin kungiyar Tsaro ta NATO. Sai dai kuma yadda ya ke furta kalamai da ba su da ce da diflomasiyya ba, su kan haifar da yamusti. Misali bayan harin da Israila ta kai wa Iran a ranar 13 ga watan Yuni, Merz ya ce: "Wannan shi ne irin mummunan aikin da Israila ta ke yi ga dukkanin mu, mu ma lamarin wannan gwamnatin yana shafar mu. Haka ma wannan gwamnatin ta 'yan Mullah ta jawo kashe-kashe da barna a duniya, ta hanyar hare-hare da kisa tare da Hizbullah da Hamas." A wajen manufofin cikin gida kuwa, batun 'yan gudun hijira shi ne kan gaba tun kafuwar sabuwar gwamnatin.
Karin Bayani: Friedrich Merz na CDU zai kasance shugaban gwamnati
Ministan cikin gida Alexander Dobrindt na jam'iyyar CSU na son rage yawan 'yan gudun hijira ta hanyar datse mutanen da ke shigo wa tun daga kan iyaka tare da kin karbar masu neman mafaka, abin da manazarta suka ce ya saba da dokokin kungiyar Tarayyar Turai. Bayan da Jamus ta dawo da binciken kan iyakoki tsakaninta da Poland, ita ma Poland ta mayar da martani da tsaurara tsaro a nata iyakokin. Wani binciken jin ra'ayin jama'a da DW ta gudanar a titunan Berlin a makon da ya gabata, ya nuna irin yadda mutane suka ga kamun ludayin sabuwar gwamnatin. Wani matashi ya ce ana samun ci-gaba, ina fata za ta ci gaba da haka. Yayin da wata matashiya kuma ta ce, ita ba ta zabi Merz ba kuma a gaskiya ba za ta zabe shi ba. Wani magidanci kuwa cewa ya yi irin sabbabin basussukan da gwamnatin ta ciwo, yana ganin babu kyau a saba alkawuran da aka yi kafin zabe.