Jamus: Kudirin tsaurara dokar shige da fice
January 31, 2025Wannan kudiri da ya tanadi rufe kofofin Jamus ga baki da masu neman mafaka da ba su da izinin shigowa kasar na jeka na yi ka ne, amma zai iya kasance wa shugaban gwamnati mai barin gado Olaf Scholz muhimmin maudu'i na yakin neman zabe mai zuwa na ranar 23 ga Fabrairun 2025. Tuni ma Scholz ya yi amfani da hira da ya yi da gidan talabijin na ARD wajen zargin abokin hamayyarsa Friedrich Merz da ke takara a jam'iyyar CDU/CSU da rusa tsohon alkawari da ya tanadi shata iyaka a siyasance da jam'iyyar Alternative für Deutschland da ke da tsattsauran ra'ayi.
"Dukkan mu mun yi asara, saboda wannan wuce makadi da rawa ne. Watakila rana ce mai matukar sarkakiya a tarihin Jamus. Ina fatan ba za a ci gaba da tafiya a kan wannan turba ba, domin wannan yarjejeniya ce da muka cimma a duk fadin kasar tun bayan yakin duniya. Tun lokacin da muka dawo da mulkin dimukuradiyya a Jamus, mun amince cewa ba za a samu hadin kai tsakanin jam'iyyun dimukuradiyya da masu tsattsauran ra'ayi ba. A yau abin da ya faru ke nan."
Ita dai majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da kudurin da CDU/CSU ta gabatar na tsaurara manufofin neman mafaka, bisa rinjayen kuri'un CDU/CSU da FDP da AfD da na ‘yan majalisa masu zaman kansu. Wannan ya faru ne saboda tun bayan rugujewar kawance tsakanin jam'iyyun SPD da Greens da FDP a watan Nuwamban bara, shugaban gwamnati Olaf Scholz ya rasa rinjaye a majalisar dokoki. Saboda haka ne kafin kada kuri'a kan kudirin shige da fice, madugun adawan Jamus Friedrich Merz ya nuna halin ko in kula game da jam'iyyun da za su kada kuri'a. amma daga bisani ya nuna damuwa game da goyon bayan da ya samu daga jam'iyyar AfD mai kyamar baki wajen samun rinjaye.
Karin Bayani: Olaf Scholz ya caccaki manufofin Merz na bakin haure
"Aikin hadin gwiwa, hadin gwiwa ne, ba kada kuri'a ba ne wanda wasu suka amince ko kuma ba su yarda ba. Ba mu yi magana da AfD ba, ba ma tattaunawa da su. Ba ma bambanta kudurori, amma muna kawo abin da muke ganin ya dace a kan al'amarin da ya yi daidai. Na biyu kuma ban yi amfani da kalmar kariya ba - watakila kun lura da haka, ba na son wutar da ke bayan bango ta zama wutar daji a daukacin Jamus."
Sai dai wannan ya saba da manufofar da jam'iyyar CDU mai ra'ayin rikau ta zartar a 2018 na kin amincewa da hadin gwiwa da jam'iyyun da ke da tsattsauran ra'ayin siyasa ciki har da Die Linke da AfD. Kazalika bayan da gwamnatin kawance ta ruguje a watan Nuwamban bara, Friedrich Merz ya yi alkawarin cewa ba zai gabatar da wani kudirin doka da AfD za ta iya taka rawa kafin sabon zaben 'yan majalisar dokokin tarayya ba.
Karin Bayani:Yan siyasar Jamus sun caccaki Musk kan AfD
Amma a hakikanin gaskiya, kudirin na shige da fice ba zai sauya manufofin mafaka na gwamnatin tarayyar Jamus ba saboda na jeka na yi ka ne. Amma dai yana bayyana ra'ayi mafi rinjayen 'yan majalisar dokoki na tarayya. Sai dai a wannan ranar Jumma'a (31.01.2025), akwai ci-gaba kan dokar da ta shafi manufofin mafaka, wanda CDU da CSU suka gabatar a majalisar dokoki ta Bundestag. Sai dai a wannan karon ma, jam'iyyun FDP da AfD mai kyamar baki da jaririyar "Bündnis Sahra Wagenknecht" (BSW) suna taka rawar gani kamar yadda suka yi alkwari.
An shafe shekaru ana zazzafar muhawara a Jamus kan shingen da ke tsakanin jam'iyyun da ke mulki da masu tsattsauran ra'ayin siyasa, da kuma yaushe za a fara hada gwiwa da su wajen kafa gwamnati. Sai dai, an dade ana samun hadin gwiwa da jam'iyyar AfD a jihohin gabashin Jamus a matakin gundumomi, inda jam'iyyar CDU ke yawan hada karfi da AfD wajen samun rinjaye. Wani bincike ya nunar da cewa sau 120 ne aka samu hadin gwiwa da AfD mai kyamar baki a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.
Karin Bayani: Merkel ta soki Merz kan hadin kai da AfD
Tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel, wacce ba kasafai take yin tsokaci kan abin da ke faruwa a fagen siyasa ba tun bayan da ta yi ritaya a 2021, ta fitar da wata sanarwa, inda ta soki matakin Friedrich Merz tana mai cewa " ba daidai ba ne a gwama kuri'un jam'iyyarsu ta CDU da na jam'iyyar AfD wajen samun rinjaye a karon farko" cikin tarihi. Sai dai kididdigar jin ra'ayin jama'a da tashar talabijin ta ZDF ta gudanar ta nunar da cewar kashi 47% na Jamusawa sun goyi bayan tsarin CDU/ CSU na samun goyon bayan AfD, yayin da kashi 48% suka yi tir da hada gwiwa wajen samun rinjaye. Amma kashi 71% sun amince cewa jam'iyyar AfD mai kyamar baki na barazana ga dimukuradiyya.