Jamus: Hukunci kan masu cin zarafin yara
July 2, 2020Talla
Ministan shari'a ta Jamus Christine Lambrecht ta jaddada aniyar gwamnati ta inganta kare rayuwar yara ta hanyar hukunci mai tsanani kan wanda aka samu da laifin lalata da kananan yara, yanzu haka dai ministar za ta jagoranci taron karawa juna sani na alkalai da masu gabatar da kararrakin lalata da yara da kuma cin zarafi.
Gwamnatin Jamus ta kebe hukuncin shekaru 15 a gidan yari ga wanda aka samu da laifin cin zarafin yara. A farkon wannan mako ne masu binciken laifuka suka ce sun yi nasarar samun shaidun da za su tabbatar da samuwar dubunnan batagarin da ke da hannu a ayyukan yada hotuna da bidiyon batsa a Internet.