Jamus da EU na taro kan dakatar da rikicin Isra'ila da Iran
June 20, 2025Ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul, ya bukaci Iran ta mayar da hankali kan cimma yarjejeniyar dakatar da shirinta na mallakar makamin nukiliya, a wani mataki na kawo karshen yakinta da Isra'ila.
Jawabin ministan na zuwa ne gabanin taron da kungiyar tarayyar Turai za ta gudanar a wannan Juma'a a birnin Geneva na kasar Switzerland, don tattauna wa da jami'an Iran domin cimma yarjejeniya.
Baya ga Mr Wadephul, sauran mahalarta taron sun hada da ministocin harkokin wajen kasashen Faransa da Burtaniya da na Iran Abbas Araghchi, sai kuma babbar jami'ar diflomasiyyar EU Kaja Kallas.
Wannan dai na zuwa bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa nan da makonni biyu zai yanke shawarar ko Amurka za ta shiga yakin Iran kai tsaye, don tallafa wa Isra'ila.
Isra'ila ta sanar da cewa sojojinta sun kai hare-hare da dama kan sansanonin sojin Iran a birnin Tehran cikin dare, ciki har da cibiyar bincike da nazarin harkokin tsaro ta SPND, wadda ke taka gagarumar rawa wajen bunkasa makamin kare-dangi na nukiliya.
A wani labarin kuma rahotanni sun nuna cewa wurare da dama sun kone a kudancin birnin Beer Sheva na Isra'ila, inda aka hango wuta na ci, har zuwa kusa da ofishin kamfanin sarrafa na'urori na Microsoft, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta rawaito.
Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce Iran na ci gaba da kai mata hare-haren makamai masu linzami har zuwa wannan Juma'a, wannan dalili ne ya sanya kasar ankarar da al'ummarta don neman mafaka, ta hanyar kada jiniyar gargadi, musamman a yankin kudancin kasar.
Karin bayani:Ko za a sulhunta Isra'ila da Iran nan kusa?
Sanarwar da Isra'ila ta wallafa a dandalin Telegram, ta ce garkuwar tare hari ta sararin samaniya ta kakkabo jirage marasa matuka da Iran ta harba mata, kuma jami'an agaji na sintiri a yankunan da aka kai wa hari da makamai masu linzami, don tallafa wa jama'a.
Mako na biyu kenan da barkewar wannan rikici tsakanin Iran da Isra'ila abokan gabar juna.