SiyasaJamus
Jamus: Ana kara samun cin zarafin mata
April 2, 2025Talla
Ministar cikin gida ta Jamus Nancy Faeser ta baiyana karuwar cin zarafin mata a Jamus da cewa babban abin damuwa ne kwarai.
Ta baiyana hakan ne yayin da ta ke gabatar da alkaluman kiddidiga a Berlin da aka tattara na cin zarafi.
Alkaluman sun nuna a shekarar 2024 an sami karuwar cin zarafi kuma ya fi yin kamari ne musamman a tsakanin matasa.
Ko da yake alkaluman sun gaza a kan na shekarar 2023, an danganta karuwar cin zarafin na baya bayan nan ga dokar da aka amince da ita a watan Afrilun bara ta sassaucin halasta shan tabar wiwi.