Jam'iyyar Greens za ta tattauna kan kudin tsaron Jamus
March 11, 2025Jam'iyya mai rajin kare muhalli ta The Greensa Jamus ta ce kofofin tattaunawarta a bude suke a kan kudin da ake shirin kashewa a kan tsaro da kuma manyan ayyuka a kasar.
To sai dai kuma shugaban Jam'iyyar Felix Banaszak ya fada a ranar Talata cewa Greens na jiran ganin kudurin da wasu jam'iyyun suka gabatar za su mika bayan tattaunawa.
Jam'iyyar CDU/CSU na kan gaba a zaben Jamus
A makon da ya gabata ne jam'iyyun CDU da SPD masu neman yin hadaka don kafa sabuwar gwamnati a Jamus suka nuna bukatar sassauta dokokin kasar kan adadin kudi da za a iya kashewa a kan tsaro da manyan ayyuka.
CDU da SPD za su koma tattaunawa don kafa gwamnati a Jamus
Duk da yake jam'iyyar Greens ba ta cikin hadakar, amma goyon bayanta na da muhimmanci saboda kudurin ya samu tsallakewa a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag.
Jam'iyyun CDU/CSU da SPD suna tattaunawa domin kafa sabuwar gwamnati a Jamus bayan nasarar da CDU ta samu na yawan kujerun majalisar dokokin kasar.