Jam'iyyar Deby ta lashe 90% na kujerun majalisar dattawa
March 4, 2025Kotun tsarin mulkin kasar Chadi ta tabbatar da nasarar da jam'iyya mai mulki ta samu a zaben farko na majalisar dattawa na watan Fabrairu, inda ta ce MPS ta lashe kujeru 43 daga cikin 46 da majalisar ta kunsa. Sai dai kotun ta amince da hujjojin da wasu jam'iyyun kawance na RNDT-Le réveil da URD suka shigar gabanta kan kwangen kuri'u, inda ta ba su kujeru biyu ko uku da ta karbo daga hannun jam'iyyar MPS mai mulki.
Karin bayani: Chadi: Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a mulkin Deby
'Yan adawa sun kaurace wa zabukan da aka shirya a Chadi saboda rashin sahihanci tun bayan da Mahamat Deby mai shekaru 40 ya tube kaki domin shugabancin na fara hula. Sai dai shugaban kotun tsarin mulki Jean Bernard Padare ya yi kira ga al'ummar Chadi da su ci gaba da yin taka tsantsan da jajircewa wajen tabbatar da dimukuradiyya. Amma dai, akwai wasu karin sanatoci 23 da shugaban kasa ke da alhakkin nadawa kamar yadda doka ta tanada.