Kawancen CDU/ CSU ya gabatar da majalisar ministoci bakwai
April 28, 2025Sama da watanni biyu bayan kawancen jam'iyyun CDU/CSU samu nasara a zabukan 'yan majalisa, shugaban gwamnati mai jiran gado Friedrich Merz ya bayyana zabin jam'iyyarsa na wadanda za su rike manyan ma'aikatun Jamus bakwai, bisa la'akari da hali na durkushewar tattalin arziki, daura da karuwar masu ra'ayin kyamar baki a cikin gida.
A yayin da ake dakon jam'iyyar SPD ta gabatar da na ta jerin ministocin, tuni jam'iyyar ta Merz ta gabatar da sunan Johann Wadfephul mai shekaru 62 a matsayin ministan harkokin waje na gwamnatin da ke tafe, mutum na farko da zai rike wannan mukami daga CDU tun wajen shekaru 60 da suka gabata.
Katherina Reiche na cikin sauran ministocin wadda za ta kula da tattali, kana Alexander Dobrindt a matsayin ministan kula da harkokin cikin gida.