Jam'iyyar CDU/CSU na kan gaba a zaben Jamus
February 23, 2025
Cikin annashuwa da murmushi ne madugun adawa Friedrich Merz mai shekaru 69 ya kada kuri'a a Arnsberg, wani gari da ke yammacin Jamus. Shi kuwa abokin hamayyarsa Olaf Scholz ya kada kuri'arsa a Potsdam da ke kudu da Berlin. Sama da masu kada kuri'a miliyan 59 ne ke da damar zabe har zuwa karfe shida na Yamma,.
Karin bayani: Sabbin manufofin ketare na taka rawa a zaben Jamus
Wannan zabe zai bai wa kasa mafi karfin arziki a Turai damar kafa sabuwar majalisar dokoki domin tunkarar kalubalen da ke girgiza tsarinta tare da haddasa damuwa a tsakanin al'umma. Ko da Daniel Hofmann mai shekaru 62 da ke da zama a Berlin sai da ya ce "Muna cikin wani yanayi mara tabbas", bayan da ya fito daga runfar zabe. A cewarsa, Jamus na bukatar "sauyi", sakamakon halin da yanayin tsaro ke ciki a nahiyar Turai sakamakon yakin Ukraine.da ake fama da shi.
Dama dai, koma bayan tattalin arziki da kuma barazanar yakin kasuwanci da Amurka da tangal-tangal da kawancen kasashen yammacin duniya a karkashin NATO ke yi na daga cikin muhimman batutuwa da shugaban CDU/CSU mai ra'ayin mazan jiya Friedrich Merz ke niyar magancewa idan ya lashe zabe. Dama ana ganin cewar zai iya zama shugaban gwamnatin Jamus na gaba, tare da juya babin dan takarar jam'iyyar SPD wato Olaf Scholz..
Karin bayani:Muhawara mai zafi gabanin zaben Jamus
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewar, Alternative na Jamus (AfD) na iya samun kashi 20%, lamarin da zai iya ninka kason da ta samu a zaben 2021. Wannan jam'iyyar da ke kyamar baki da kuma ke dasawa da Rasha ta sanya jigogin maudu'an yakin neman zabenta kan munanan hare-hare da 'yan kasashen waje suka kai a kasar Jamus. Sannan zaben ‘yan majalisar dokokin Jamus na gudana ne a jajibirin cika shekaru uku da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. Rikicin ya yi sanadin katse iskar gas da Rasha ke samarwa a kasar.
A tsarin zaben majalisar dokokin Jamus, ana iya daukar makonni ko ma watanni kafin a kafa sabuwar gwamnati. Hasali ma, don kafa kawancen gwamnati, jam'iyyar CDU/CSU mai ra'ayin rikau za ta iya zawarcin jam'iyyar Social Democratic Party (SPD), bayan da ta haramta wa kanta kawance da AfD mai kyamar baki. Sai dai idan jam'iyyar SPD mai mulki a yanzu ta samu kashi 15% na kuri'un da aka kada, wannan sakamakon zai zama mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu. Amma dai, rabon kujerun majalisar Bundestag zai dogara ne da sakamakon da kananan jam’iyyun siyasa za su samu.