Jam'iyyar APC ta kauce wa barazana ga makomarta
February 26, 2025Duk da cewar an dauki lokaci ana musayar yawu har ma an kai ya zuwa tashin kura, masu tsintsiyar tarayyar Najeriya, sun kare wani babban taro tare da kauce wa rikicin da aka dauki lokaci ana ta hasashe.
Tsoron rikicin ne dai ya kai uwar jam‘iyyar gaza kaiwa ya zuwa babban taron shekaru biyu bayan babban zabe na kasar.
To sai dai kuma daga dukka na alamu ta mazar Gandujen da ma abokan taku na shirin biya na bukata ga shugaban kasar da ya kare taron da karuwar tagomashi tsakanin yan jama'iyyar.
Kama daga shi kansa Tinubun ya zuwa Gandujen dai an kare taron tare da yaba wa kokarin su na kaiwa zuwa hadin kai da kila ci gaban da ke cikin jam'iyyar.Babu dai daya a cikin yan tawayen da mafi yawansu ke zaman jami'ai na tsohuwa ta gwamnatin kasar cikin zauren taron.
Duk da goron gaiyyar da a cewar shugaban jam'iyyar Abdullahi Umar Ganduje suka mika bisa jagoran rikicin dama makarabbai.
Tafiya a karkace ga masu tsintsiya ko kuma fada na kaiwa baki na a ci, da kamar wuya goyon bayan ya haura laraba cikin satin rikici.
A baya dai cikin tarihi bita da kulli kan biyu tafawa cikin rigingimu na siyasa.
To sai dai kuma irin nasarorin Gandujen na shirin zama na kariya a gare shi a tunanin Sanata Barau Jibrin da ke zaman mataimaki na shugaban majalisar dattawa ta kasar.
Koma ya zuwa ina tsintsiyar take shirin ta kai madauri a daya, majiyoyin taron dai sun ce fadar gwamnatin kasar ta na neman hanyar lallashi bisa korafi na masu neman a fasar.
Kuma a lokaci na kankane ake saran kai wa ya zuwa fitar da jeri na mukamai da nufin kwantar da hankula da kila ma neman hanyar damar sake komawa filin dagar cikin cikkake na hadin kan.
Sanata Mustapha Salihu dai na zaman jigon jam‘iyyar daga sashen arewa ta tsakiya, sashen kuma da suka yi asara ta shugabancin jam'iyyar. Kuma yace dabara ta siyasa ce ta sa su kaiwa ya zuwa maida wuka cikin kuben.
APC dai na a tsakanin mantawa da batun rikicin cikin gida da nufin cika alkawarin da ke tsakaninta da miliyoyi na yan kasar, kuma kai wa ya zuwa ga turjiya a lokaci na kankane.