Jam'iyyar adawa ta sahale wa Lee Jae-myung takararta
April 27, 2025Jam'iyyar Democrat mai adawa a Koriya ta Kudu, ta tsayar da Lee Jae-myung a matsayin dan takararta a zaben gabanin wa'adi na shugaban kasar, da za a gudanar a farkon watan Yuni mai zuwa, bayan tsige shugaba Yoon Suk Yeol daga madafan iko.
Tsohon shugaban Kotiya ta Kudu yana ficewa daga fadar gwamnati
Kaso fiye da 89 cikin 100 ne dai suka kada kuri'ar na'am da takarar Mista Lee, a jam'iyyarsa ta masu matsakaicin ra'ayi, kana a jawabin da ya gabatar jim kadan bayan wannan nasara, dan takarar ya ce ba zai ba wa marada kunya ba. Mai shekaru 60 a duniya Lee Jae-myung, ya ce yana da fata na sake shata wata makoma mai cike da tarihi.
Kotu ta amince da tsige shugaban Koriya ta Kudu
inda yace "Al'ummar Koriya ta Kudu da 'yan jam'iyyata sun ba ni damar da za ta kai ga shata wata Koriya ta Kudu sabuwa mai cike da 'yanci da walwala da kuma gaskiya." Za a gudanar da zaben shugaban kasa ne a Koriyar ta Kudu nan da makwanni biyar masu zuwa domin maye guirbin Shugaba Yoon da aka tsige bayan ya ayyana dokar tabaci a kasar.