Jami'an Ukraine da na Rasha za su gana a Turkiyya
June 1, 2025Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa tawagar jami'ai daga kasarsa za ta halarci birnin Santabul na Turkiyya a gobe Litinin, domin ganawa kai tsai da jami'an Rasha kan kokarin sulhunta rikicin kasashen biyu ta hanyar diflomasiyya.
Sai dai a lokacin da yake sanar da karbar goron gayyar, Shugaba Zelensky ya ce ya riga ya zayyana matsayarsa a game da zaman tattaunarwar, sannan kuma ya bayyana sunan Rustem Oumerov a matsayin wanda zai jagoranci tawagar Ukraine kamar a zaman taro na farko da aka yi a watan Mayu da ya gabata.
Karin bayani: Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni
Zekensky ya kuma kara da cewa muhimman abubuwa da Ukraine ta sa a gaba su ne cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da kuma sakin fursononi da dawo da yaran Ukraine da Kyiv ke zargin Moscow da sacewa a lokacin ta kaddamar da mamaya.