Jami'an tsaro sun afka wa masu zanga-zanga a Amurka
June 8, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya aika da jami'an tsaro 2,000 zuwa birnin Los Angeles don shawo kan tarzoma da aka yi saboda kame bakin haure ba bisa ka'ida ba.
Shugaban harkokin kan iyaka a gwamnatin Trump, Tom Homan ya shaida wa gidan talabijin Fox News ranar Asabar burinsu shi ne Los Angeles ya zama birni mafi aminci.
Jihar California da birnin na Los Angeles ke cikinta dai ta sha gamu da tarzoma na biyu a ranar Asabar, inda mazauna wata unguwa da galibinta 'yan Latin ne suka yi arangama da jami'an hukumar kame bakin haure, ICE.
An yi amfani da barkonon tsohuwa da ma sanduna don tarwatsa tarukan mutane a unguwar Paramount.
A cikin wannan makon, an kama mutane 118 a Los Angeles, ciki har da 44 a ranar Juma'a.
Gwamnan jihar California Gavin Newsom ya yi Allah wadai da kamen, yana mai cewa babu tausayi a ciki.